1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya mai sana'ar walda a Bauchi

Muhammad Waziri Aliyu LMJ
April 15, 2020

Wata matashiya a jihar Bauchi da ke Najeriya, ta kama sana'ar walda, inda ta ce da wannan sana'ar ta dauki nauyin karatunta har ta kammala.

https://p.dw.com/p/3aw8O
Flash-Galerie Art Entreprise
Hoto: Chris Spatschek

Matashiyar ta ce bayan da ta kammala karatun nata, ta ci gaba da sana'arta ta walda ba tare da jin cewa ta fi karfin yin ta ba, duk kuwa da matakin karatun da ta samu. Matashiyar dai na da wasu matasa maza a karkashinta da suma ke samun na sawa a bakin salati cikin sana'ar ta walda. 

Ita dai sana'ar walda musamman ma a arewacin Najeriya, an fi sanin maza da ita, amma duk da haka wannan bai hana Rabi'atu Muhammad dagewa wurin ganin ta kware cikin sana'ar ta walda ba, duk kuwa da irin matsalolin da ta yi ta cin karo da su yayin koyon sana'ar. Wannan ne ma ya sanya jama'a ke mata kirari da mace mai kamar maza saboda kwazonta a bakin aikinta. 

Wasu daga cikin matasan da ke aiki a shagon Rabi'atu sun bayyana cewa ganin rashin alfanun zama haka ba tare da motsawa domin neman na kansu ba, shi ne dalilin da ya sanya suka koyi aikin waldar kuma suke alfahari da ita kasancewar ta musu riga da wando.