Hillary Clinton ta yi bayani kan harin Benghazi
October 22, 2015A Amirka a wannan Alhamis Hillary clinton 'yar takarar neman shugabancin kasar a zabe mai zuwa kana tsohuwar sakatariyar harakokin wajen kasar na bayyana a gaban majalissar dokokin kasar domin bayar da bahasi kan batun harin da wasu 'yan ta'adda suka kai wa ofishin jakadancin kasar ta Amirka a birnin Benghazi na kasar Libiya a ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2012. Harin da ya yi sanadiyyar mutuwar jakadan kasar ta Amirka Chris Stevens da wasu jami'an Kungiyar Leken Asirin kasar ta Amirka ta CIA biyu da wani ma'aikaci ofishin jakadancin guda.
Tsohuwar sakatariyar harakokin wajen kasar ta Amirka za ta bayyana a gaban komitin musamman da 'yan majalissar dokokin jam'iyyar Republican ta masu rinjaye suka kafa a bara domin gudanar da bincike kan wannan hadari wanda jam'iyyar adawa ta 'yan Demokrate ke amfani da shi wajen yin muguwar farfaganda ga Hillary Clinton wacce ke neman tsayawa takarar neman shugabancin kasar ta Amirka a zabe mai zuwa na shekara ta 2016 .