Hillary Clinton ta nuna sha´awar zama macen farko a mukamin shugabar Amirka
January 21, 2007Talla
´Yar majalisar dattijan Amirka kuma uwargidan tsohon shugaban kasar, Hillary Clinton ta dauki matakin farko na kaddamar da wani kamfen na zama mace ta farko a mukamin shugaban Amirka. A cikin wani sakon faifayen bidiyo aka watsa ta shafin ta na intanet, Hillary Clinton mai shekaru 59 ta gaiyaci masu kada kuri´a da su fara tattaunawa da ita akan manyan batutuwa da kasar ke fuskanka. A kuma halin da ake ciki gwamnan jihar New Mexico Bill Richardson ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar ta Amirka. Richardson wanda shi ma dan jam´iyar democrat ne ya ce zai kafa wani kwamiti don yin duba hanyoyin samun nasararsa.