1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Hezbollah ta kai hari a kan Isra'ila bayan tsagaita wuta

Mouhamadou Awal Balarabe
December 2, 2024

Kungiyar da ke samun goyon bayan Iran ta kai hari a kan tsaunin Kfar Chouba, lamarin da ya sa Isra'ila ta sha alwashin mayar da martani, a daidai lokacin da suke zargin juna da karya yarjejjeniyar tsagaita bude wuta.

https://p.dw.com/p/4nf87
Wannan ne tsaunin Kfar Chouba da Hezbollah ta kai hari bayan cimma tsagaita wuta
Wannan ne tsaunin Kfar Chouba da Hezbollah ta kai hari bayan cimma tsagaita wutaHoto: Mohammad Zaatari/AP/picture alliance

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa ta kai farmaki kan wani sansanin sojin Isra'ila, a karon farko tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninsu ta fara aiki.  A cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin Beyrouth, kungiyar da ke samun goyon bayan Iran ta bayyana cewa ta kai hari kan tsaunin Kfar Chouba da Lebanon ke ikirarin cewa mallakinta ne amma Isra'ila ta mamaye.

Karin bayani:  Hezbollah da Isra'ila sun cimma yarjejeniya

Sai dai sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa Hezbollah sun harba makamai masu linzami guda biyu a sansaninsu. Saboda haka ne gwamnatin Isra'ila ta sha alwashin mayar da martani kan Hezbollah, a daidai lokacin da bangarorin biyu ke zargin juna da karya yarjejjeniyar tsagaita bude wuta. Kakakin majalisar dokokin Lebanon Nabih Berri ya yi ikirarin cewa Isra'ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta akalla sau 54 cikin mako guda. Sai dai fadar mulki ta Tel Aviv ta yi watsi da zargin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta.