Helmut Kohl - Mutumin da ya kafa tarihi
Kusan rayuwarsa ta siyasa ta kawo karshe a 1989, amma sai tarihi ya sauya, Helmut Kohl ya yi amfani da wannan dama. Manufar siyasarsa a Jamus da Turai na zama abinda aka gada daga shugaban gwamnatin Jamus na shida.
Mai dogon buri a sana'ar da ya zaba
Tun da wuri ya san abinda yake so. Wanda ake wa lakabi da "Jikan" Konrad Adenauer, shugaban gwamnati na farko, amma bai dauki kansa a haka ba. Sai dai Kohl ya yi amfani tasirin "Dattijon". Tun yana matashi dan siyasa a jihar Rheinland-Pfalz ya gaiyaci Adenauer zuwa babban taron CDU ta jiha, ba tare da sanin Firimiyan jihar kuma dan CDU Peter Altmeier ba. Hakan ya zama wani juyin mulki daga sama.
Isashshen lokaci ga iyali?
Helmut Kohl dan zamani ne. Tun a matsayin dan siyasa na jihar Rheinland-Pfalz a farkon shekarun 1970 ya gano karfin ikon 'yan jarida. 'Yan jarida na a cikin wadanda yake yawaita karbar bakoncinsu a gidansa da ke Oggersheim. Hoton da "Uban Jiha" kuma "Maigida" ya yada a wancan lokaci na zama wanke kansa. Kohl ya kasance mai dogon buri da kwazo na wancan lokaci.
Buri ya cika, Shugaban gwamnati!
A 1 ga watan Oktoban 1982 Helmut Kohl ya cimma burinsa na siyasa. Dan siyasar daga wani lardi ya zama shugaban gwamnati inda ya maye gurbin "Dan siyasar duniya" Helmut Schmidt na jam'iyyar SPD. Lokaci ne da Kohl ya girbi yawan barkwanci daga masu ra'ayin sauyi. Sai dai da yawa sun raina kwarewarsa da jarumtarsa a fagen siyasa. A shekarun da suka biyo baya ya ja zarensa.
Wani yanayi mai cike da tarihi
Alama ga littattafan tarihi. A 22 ga watan Satumba 1984 a wata makabartar soji a kusa da Verdun. Shin wa ya fara mika ma wani hannu? Shugaban Faransa Francois Mitterrand ya kama hannun Helmut Kohl. Wannan lokacin ya kasance mai muhimmanci da ya auku a makabartar ta sojojin Jamus da Faransa. Ana kwatanta shi da sunkuyawar da Willy Brandt ya yi a Warsaw.
1989 dab da kaiwa karshe
Kiris a rufe makomarsa ta siyasa a babban taron jam'iyya a watan Satumban 1989 a Bremen. Cikin yanayi na rashin koshin lafiya, Kohl ya hana jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar CDU yi masa "juyin mulki". Jim kadan gabanin haka ya samu labarin cewa kasar Hangari za ta bude iyakokinta ga dubban 'yan gudun hijirar Jamus ta Gabas. Kasa maye gurbinsa ya bude masa sabuwar dama ta siyasa.
"Idan lokaci ya bada dama..."
A 19 ga watan Disamban 1989 ba a riga aka yanke shawara kan makomar Jamus ba. Kohl yana a birnin Dresden, jita-jita ta yadu. Yana dab da yin wani jawabi a majami'ar Frauenkirche (Church of Our Lady). Shin ya so ya bayyana fatan mutane ne? Ya yi ta jinkiri na tsawon lokaci, kafin ya fito fili: "Hadewar kasarmu ta Jamus." A gaban dubun dubatan jama'a da ke cike da doki.
Cikin kananan riguna zuwa ga hadewa
Tsakanin 14 da 16 ga watan Yulin 1990 abubuwa sun kasance kamar yadda Jamus ta so kan hadewarta. Akalla a kan "Hadewar iyakokinta". Kohl da Genscher sun je Mosko da Kaukasus, mahaifar Gorbachov. A kan batun zaman hadaddiyar Jamus cikin kungiyar NATO. Gorbatchov ya amince. Shi ne shingen siyasa na karshe kuma mafi girma a hanyar sake hadewar Jamus.
Shi ma mutum ne mai kare kansa
Helmut Kohl bai taba rasa karfin kare kai ba. Ana kiransa "Dogo kakkaura", a saboda tsayinsa na mita 1.93 da kuma alkiblarsa ta siyasa, yana iya kare kanshi da kanshi. Masu tsaron lafiyarsa na jin jiki wajen tsayar da mai ba su umarnin a zangon da ya kamata ya tsaya, kamar yadda ya faru a ranar 10 ga watan Mayu lokacin da masu zanga-zanga suka jefe shi da kwai a Halle.
Hadaddiyar Jamus a Turai
Turai ba kawai ta kasance babban fagen siyasar Helmut Kohl ba ne, ta kuma zama abinda ke zuciyarsa a kullum. An kammala batun hadewar Jamus, amma ba a yi bikin sake hadewar ba, lokacin da Shugaban Hukumar EU Jacques Delors ya ba wa Kohl taswirar Turai lokacin wata ziyara a Bonn. Hadaddiyar Jamus a matsayin memba.
Wani sha'ani na iyali
A shekarar 2001 Hannelore Kohl ta kashe kanta bayan rashin lafiya na tsawon lokaci. Mutuwarta ta gurgunta iyalin. Domin Kohl dan siyasa da Kohl magidanci ya koma bayan fage. „Ban wuce iyaka ba, idan na fada muku cewa rayuwa ta bainar jama'a da mahaifina ya yi ta yi tasiri har zuwa matakin karshe a gida“, inji dansa Walter a cikin littafin da ya wallafa.
Mutane masu muhamminci ga Kohl
Yana tuna wa da duk wanda ke da muhmmanci a gare shi. Ita ma Angela Merkel ta dauki hankalinshi tun tana matashiya. A matsayin "Yarinyar Kohl" ta samu alfarmarsa a lokaci mai tsawo. Amma sun nesanta da juna bayan da Kohl ya ki bayyana wadanda suka tallafa wa CDU da miliyon kudi. Wasiyar Kohl ta karshe ta yi watsi da jawabin Merkel a wani taron kasar Jamus.
Maike Richter-Kohl
Tun 2005 take tare da Kohl sun yi aure shekaru uku baya, ita ce matar da ke gefenshi. 'Yar shekaru 53 masaniyar tattalin arziki, ana zarginta da neman amfani da martaba da girmar Kohl don cimma burinta. Ana kuma zarginta da zama musabbabin raba gari da aka yi tsakanin Kohl da 'ya'yansa biyu maza. "Ita ke kula tana kareshi tana kuma iko da shi", inji jaridar Süddeutsche Zeitung tun a 2012.
Kungiyar EU ta girmama Helmut Kolh a Strasburg
Shugabannin kasashe da dama ne na kasahen kungiyar tarrayar Turai suka hallara a birnin Strasburg na Faransa, inda suka yi ban kwana na karshe da tsohon shugaban kasar wanda aka ajiye gawar sa a zauran majalisar wanda aka girmama. A cikin shugabannin har da shugabar gwamnatin Jamus da shugaban Faransa da na Spain. Helmut Kohl ya kasance jagora na hadewar Jamus, ya kuma mutu yana da shekaru 87.
An zagaya da gawar Helmut Khol a garin Ludwigshafen
An zagaya da gawar tsohon shugaban na Jamus a garin Ludwigshafen inda nan ne mahaifar sa da ke a Jihar Rheinland Pflaz da ke a yammacin Jamus idan jama'a suka yi ban kwana na karshe da tsohon shugaban wanda ya rasu yana da shekaru 87. Kafin a yi bisar sa.
An dauki gawar Helmut Khol zuwa garin Speyer
An dauki gawar Helmut Khol cikin jirgin ruwa don kai ta a garin Speyer idan nan ne aka tsara za a binne shi a wata makabarta da ke a birnin bayan an yi masa adu'oi a cikin wata majami'ar.
Jana'izar Hemut Khol a garin Speyer
Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus,da shugaban Jamus Frank Walter Steinmeier da shugaban majalisar dokokin kasar Bundestag Norbert Lammert tare da sauran jama'ar sune ke tsaye a gaban gawar a cikin wata majami'ar da ke a garin Speyer inda aka binne tsohon shugaban na Jamus Helmut Kohl.