1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Helen Joseph: 'Yar gwagwarmaya da ta yi kasada

December 3, 2020

An haife ta a Birtaniya da duk dama da take da ita amma Helen Joseph ta yi kasadar kalubalantar mulkin nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. DW ta tattauna rayuwarta da dan gwagwarmaya Carl Niehaus.

https://p.dw.com/p/3m6sh
African Roots | Helen Joseph

An haifi Helen Joseph ranar 8 ga watan Afrilu 1905, a kauyen West Sussex da ke Ingila, amma ta yi zamanta ne a birnin London. Bayan kammala jami'a a Ingila, ta fara aikin koyarwa a Indiya kafin daga bisani ta koma Afirka ta Kudu a shekarun 1930 inda ta auri likitan hakori da zama cikin Turawa masu galihu a Afirka ta Kudu.


Aikin da ta yi da sojoji lokacin yakin duniya na biyu ya zama abin da ya bude mata ido, amma a matsayin ma'aikaciyar jin dadi jama'a wannan ya taimaka mata fara gwagwarmaya da mulkin nuna wariyar launin fata na Afirka ta Kudu a shekarar 1952 - kuma irin wannan aikin na ma'aikaciyar jin dadi jama'a ne Winnie Madikizela-Mandela ta yi.


Tashar DW ta yi hira da Carl Niehaus, wanda shi kansa ya dade cikin gwagwarmaya karkashin jam'iyyar ANC kana tsohon mai magana da yawun Nelson Mandela, game da rayuwar Helen Johnson.

DW: Yaushe ka gamu da Helen Joseph?
Carl Niehaus: Na gamu da Helen Joseph lokacin ina shekaru 19 da haihuwa kuma ta zama daya daga cikin mutanen da suka horas da ni batun siyasa a rayuwa.


Wace irin mata ce Helen Joseph?
Tana da ka'ida ta kuma mika wuya kan kare hakkin dan Adam. Addinin Kirista ya yi tasiri a rayuwarta cewa duk mutane Ubangiji ne ya halicci da dama iri guda. Tana da yakinin cewa dole a yi adawa da tsarin nuna banbancin launin fata. Domin haka ta shiga jam'iyyar Congress of Democrats wadda ke da dangantaka da jam'iyyar ANC.


An raba dangantaka tsakanin ANC da sauran jam'iyyun al'ummomi domin tabbatar da kowa ya samu nasara daga bangarori al'umma. Me ya sa hadakar ta ba ta damar jagoranci?
Saboda tana iya nuna inda aka dosa haka ya janyo ta zama daya daga cikin shugabannin. Ta samu damar gabatar da kudiri kan 'yanci lokacin taron mutane a Kliptown da ta jagoranci macin mata wanda ya yi suna a shekarar 1956.

African Roots | Helen Joseph


Ranar 9 ga watan Satumba 1956, mata dubu 20 sun nuna takaici kan mulkin nuna wariyar launin fata, daya daga ciki shi ne takaita zirga-zigar jama'a da damar yin aiki gami da kula da iyalai. Tare da bakake gami da sauran 'yan Indiya, Helen Joseph ta jaroranci macin mita takardar koke ga ofishin Firaminista J. G. Strijdom. Mene ne wasu daga cikin bukatun matan?
Ta yi imani cewar dole ne mata su yi gwagwarmaya. Ta gamsu masu cin zarafin mata sai sun fuskanci hukunci.


Yaya aka yi wannan Baturiya da aka haifa a Ingila ta saje da masu gwagwarmayar kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata?
Ta mika wuya kan samun mutane da babu banbancin launin fata da samun Afirka ta Kudu bisa 'yanci ga kowa. Ita ce mutum mara nuna banbancin launin fata da na sani.


Ganin tana da shekaru 40 lokacin da aka fata mulkin nuna wariyar launin fata, Helen Joseph tana cikin mutane na farko da suka fara gwagwarmaya. Me kake tunawa game da ita?
Na gamu da ita lokacin tana shekarunta 70. Duk da haka tana karfin gwiwa da shiga gwagwarmaya kan yaki da mulkin nuna wariyar launin fata. Wannan lokacin ne aka garkame ta a gida da ke Northcliff a Johannesburg kusan shekaru biyar.


Tsarin ba ya sassauci ga Turawa da suna nuna adawa. Ka ga lokacin da Helen Joseph ta fuskanci amfani da karfi?
Akwai lokutan da masu nuna wariyar launin fata suka bude wuta a gidanta duk da ta tsufa kuma babu mai kare ta. Zan iya tunawa wata rana da safe bayan faruwar irin wannan lamari na isa gidanta na samu tana kan share gilashin da ya fashe bayan an yi harbi da taga. Idanunta sun fiffito. Ranta ya baci, tana cewa ''za su kashe mu, amma ba za su iya kashe manufar da muke da ita ba ta tabbatar da 'yanci a wannan kasa''.
Haka na tuna lokacin da ta kawo min ziyara bayan an kama ni. Ta zo wajen shari'ar tana zaune a gaba na keke guragu.


A gidanta kullum tana tambayata na tsuguna a gabanta ta adaya bangaren teburin daki. Tana maganar nuna rashin jin dadi da nuna wariyar aunin fata. 
Wadane lokuta na gwagwarmayar za ka iya tunawa game da ita?
Ta tabbatar da cewa wadanda aka daure da iyalansu ana tunawa da su. Kowane lokacin Kirsimeti tana shirya liyafa, masu gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata suna biki a gidanta tare da tunwa da wadanda suke gidan fursuna. Kuma da kare 12 na tsakiyar dare "Ake tunawa da wadanda suke daure.”

Helen Joseph 'yar gwagwarmaya da nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu


Me kake tunawa lokacin da Helen Joseph ta yi kusan mutuwa?
'Yar gwagwarmaya ce har ta mutu. Ina gefen gadon da ta mutu, ranar Kirsimeti da karfe 12 na rana. Ta rasu a asibitin birnin Johannesburg wanda yanzu aka saka masa sunan ita Helen Joseph.


Wannan a shekarar 1992, lokacin da fara daura Afirka ta Kudu kan tafarkin dimukuradiyya. Saka sunan asibitin daga J. G. Strijdom a shekarar 1997 ya nuna nasarar da ta samu kan tsohon firaministan da ta jagoranci macin mata lokacin mulkinsa, kuma girmamawa ga abokanta na gwagwarmaya. Shin duk tsawon shekarun Helen Joseph tana amincewa da 'yan gwagwarmaya?
A karshe Helen Joseph ta nuna damuwa kan yadda Shugaba Nelson Mandela da jam'iyyar African National Congress (ANC) suka nuna sassauci da wuri lokacin da aka fara tattaunawar kafa tsarin dimukuradiyya. Kuma tana ganin shirin sasantawa ya rinjayi na tabbatar da adalci.
Carl Niehaus Carl Niehaus na cikin jiga-jigan jam'iyyar African National Congress (ANC) kana mamba a shekaru 42. Yana cikin 'yan kwamitin zartaswa na tsofaffin wadanda suka yi amfani da makami na jam'iyyar ANC.


Thuso Khumalo ne ya yi wannan hira.


Wadanda suka taimaka da shawarwari wajen rubuta wannan tarihi sun hadar da Farfesan tarihi Doulaye Konaté da Dr. Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo. Gidauniyar Gerda Henkel  ce ta taimaka wajen kawo muku Tushen Afirka.