1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

HdM: Dinka kyallen rufe baki da hanci

June 11, 2020

Bullar cutar Corona-virus ta bai wa wata matar aure matashiya a jihar Kaduna da ke Najeriya damar kama sana'ar dinka takunkumin rufe baki da hanci a cikin kasuwanni.

https://p.dw.com/p/3deO1
Corona-Ausbuch in Afrika
Hoto: picture-alliance/D. Lloyd

Bullar cutar Corona-virus ta baiwa wata matar Aure matashiyar kaduna damar kama sana'ar Dinka kyallen rufe fuska da ake saida mata a cikin kasuwannin kaduna dan rufawa kanta da mijinta har ma da kishiyarta asiri. To Karar keken Dinkin wata matashiya matar aure kana matashiya mai suna Khadijar Labaran da ke zaune a wani kauyen Hayin Kogin Kaduna, da ta kama sana'ar dinka kyallen rufe baki da hanci dan rufawa kanta asiri da mijinta tare da kishiya, a cewar ta dai zuwan cutar coronavirus ya ba ta wata damar samun taikamawa iyalenta ta hanyar dinka kyallen rufe fuskanta da sauran dinke-dinke

Khadijah Labaran ta bayyana cewa wannan sana'ar na kyallen rufe baki da hanci na taimaka masu ta hanyoyi masu yawa wanda ya kunshi yadda suke samun damar biyan kudin makarantar ‘ya'yansu. Daga cikin nasarorin da ta samu dai sun hada da irin ci-gaban da take samu wajen fadada sana'arta, da kuma yadda manya da kananan ‘yan kasuwa ke zuwa sayan kayayyakin dinki. A kokarin ba da taimakon ganin yaki da yaduwar cutar Covid-19.