1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashiya mai kujeru da tayoyin abin hawa

November 10, 2021

Wata matashiya a jihar Kaduna da ke Najeriya, na amfani da tsofaffin tayoyin motoci da babura wajen yin kujeru na zamani.

https://p.dw.com/p/42oj5
Symbolbild Autoreifen Reifen Gummi
Amfani da tsofaffin tayoyi wajen yin kujeru, domin dogaro da kai da kare muhalli Hoto: picture-alliance / Helga Lade Foto

Matashiyar mai suna Khadija Sa'ad dai ta rungumi wannan sana'ar ne jim kadan bayan kammala karatunta. A cewarta ta yi nazari kan irin tayoyoin motoci da na a dadaita sahu da babura da ake zubarwa barkatai idan sun lalace.

Matashiya Khadija ta ce tana amfani sarrafa tayoyin wajen yin sana'a da kuma kare muhalli ganin yadda tayoyin ke gurbata muhalli da kuma yawan sare bishiyoyi domin sarrafa su wajen yin kujerun da ake yi da katako.

Khadija na koyar da sauran 'yan uwanta matasa wannan sana'a da tace ta cimma nasarori da dama da ita, koda yake ba a rasa kalubale musammman daga masu sayen kayan da wasu ke ganin ba za su iya sayen kujerun da aka yi da tsofaffin tayoyin ababen hawa ba.