1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi ya kirkiri injin abincin kaji

March 31, 2021

A kokarinsa na samarwa kansa aikinyi, wani matashin Kaduna mai baiwar kirkire-kirkiren fasahar zamani, ya kirkiro wani injin nika abincin kaji da sauran dabbobin da ake kiwo a gida.

https://p.dw.com/p/3rPVP
Eco Africa Sendung
Saukaka hanyar samar da abincin kajiHoto: DW

Matashin mai suna Abdullahi Ahmed ya ce wannan inji na da inganci da kuma juriya wajen harhada abubuwan da suka jibanci na kayan abincin kaji da sauran dabbobi, kuma yana taimakawa masu kiwon dabbobi samar da abincin a saukake. Ahamed ya ce ya kirkiro injin ne, domin bunkasa kiwon dabbobi ta hanyar cin abinci mai gina jiki yadda masu kiwo za su samu riba mai tsoka. Kayayyakin abinci daban-daban ake hadawa sannan injin ya nika kuma acewarsa, yawancin kamfanonin da ke sayar da abincin kaji da na sauran tsuntsaye a wurinsa suke saya.

Karbuwa da samun kasuwa na daga cikin Nasarorin da ya samu, buga da kari ya samarwa matasa da dama aikin yi ta hanyar wannan sana'ar. Duk da irin nasarorin da ya samu, akwai kuma manyan kalubalen da ke ci masa tuwo a kwarya, wadanda suka hada da rashin wadataccen hasken wutar lantarki da kuma rashin tallafin hukumomi da kungiyoyi da ma attajiran yankin. Matashin ya shawarci matasa a kan su tashi tsaye wajan yaki da zaman kashe wando. Fatarnsa dai a kullun shi ne, na kirkiro wani sabon abun da ka iya taimaka wa wajan inganta rayuwar dabbobi da ma dan Adam.