1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: Mai sana'ar jari bola

February 24, 2021

Wani matashi a jihar Katsina da ke Najeriya, ya kama sana'ar sayar da karafuna da aka fi sani da jari bola domin dogaro da kansa. Matashin dai ya bunkasa sana'ar, inda ya yi karatu a jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua da ita.

https://p.dw.com/p/3pncx
DW Eco Africa Plastik Recycling
Sana'ar jari bola dai na samun wajen zama musamman a NajeriyaHoto: DW

Matashin na hada-hadar sayar da karafunan ne a kasuwar kayan nauyi da ke birnin Katsina, inda ake kai masa karafunan daga bangarori dabam-dabam yana saye. Matashin mai suna  Nura Musa Kofar Kaura ya ce ya samu nasarori sosai a wanann sana'a ta sayar da karafa, inda ya ce ya fara jari bolan da daukar dan buhu yana zagayawa yana sayen karafunan har sana'ar ta bunkasa

Matasa da dama a kasar Hausa kan dogara da aikin gwamnati musamman wadanda suka yi karatun boko, abin da Nura Kofar Kaura ke cewa gurgun tunani ne. Wannan matashi dai yana ci gaba da tasawa saboda yadda sana'ar ta bunkasa, inda yanzu haka yake da shaguna hudu a kasuwar kuma ko da yaushe akwai matasa da ke kewaye da shi.