1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai sana'ar noman Dankalin turawa

March 23, 2022

Wani Matashi a jihar Katsina da ya kammala karatun HND babu aikin yi ya kama sana'ar noman rani inda ya bada karfi a noman Dankalin Turawa dan dogaro da Kai.

https://p.dw.com/p/48wki
Flash-Galerie Geschichte der Kartoffel
Hoto: BilderBox

Matashin ya fara cirar Dankalin yana kaiwa kasuwanni yana sayarwa, yace ya samu nasarori sosai kuma akwai mutanan da ke ci karkashinsa 

Matashin Abdullahi Bature yana noman rani ne a kauyen Darkama dake karamar hukumar Kaita Arewacin Birnin Katsina. Ya yi karatun injiniya kuma hakan ya bashi damar saukaka wa kansa noman ranin musamman wajan yin ban ruwa abun da yake kara tutiya da nasarar da ya samu a noman

Wannan matashi ganin irin nasarar da ya samu a sana'ar noman dankalin turawa yasa ya ja hankalin 'yan uwansa matasa da su tashi su nemi na kansu.

Matashin yace babban burinsa shine ya cigaba da fadada noman duk shekara dan karin dogaro da kai da kuma samar wa 'yan uwansa matasa abun yi.