1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haɗewar Jamus ta gabas da ta yamma

Usman ShehuSeptember 1, 2010

An yabawa Jamusawan da suka yi tsayin daka, don haɗewar gabaci da yammacin Jamus a matsayin ƙasa guda

https://p.dw.com/p/P1Pg
Helmut Kohl gwarzon hadin kan JamusHoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta yaba da namijin ƙoƙarin al'ummar tsohuwar Jamus ta gabas, inda tace ƙoƙarin nasu shine ya kai ga sake haɗewar ƙasar. Merkel tana jawabi ne a bikin cika shekaru 20 da sanya hannu kan haɗewar Jamus ta gabas da ta yamma. An sanya hannu kan ƙudurin ne shekara guda bayan faɗuwar katangar Berlin a shekara ta 1989, inda aka sake haɗe Jamus ta gabas da ta yamma a matsayin gwamnatin tarraya, a ranar uku ga watan Oktoba shekara ta 1990. Bikin ya samu halartan manyan mutane ciki har da firimiyan tsohuwar Jamus ta gabas na ƙarshe Lothar de Maiziere, da ministan harkokin wajen Jamus ta yamma a wacan lokacin Hans-Dietrich Genscher.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Eidita: Umaru Aliyu