1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa a kan kogin Nilu

Binta Aliyu Zurmi
August 16, 2020

Kasashen Masar da Habasha da Sudan da ke rikici a kan kogin Nilu wanda da ya ratsa tsakaninsu sun sake hawa teburin sulhu a karkashin jagorancin kungiyar tarayar Afirka AU.

https://p.dw.com/p/3h3Jn
Bildergalerie Nil Damm Beeinträchtigung des Flusses
Hoto: Reuters/M. Nureldin Abdallah

Da nufin kawo karshen takaddamar madatsar ruwan da Habasha ke ginawa.  A cewar sanarwar da ta fito daga jami'an Masar da Habashar.

Wannan rikici dai ya kwashe shekaru tare da janyo hankulan masu daidaita rikici ciki kuwa har da shugaban Amirka Donald Trump, amma duk da haka ba su cimma nasarar kawo daidaito ga kasashen ba.