1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen da ke gaban hafsoshin sojin Najeriya

Uwais Abubakar Idris/ZMAJuly 14, 2015

Jama'a sun zura idanu su ga kamun ludayin sabbin hafsoshin soji da shugaba Muhammadu Buhari ya nada bayan daukan dogon lokaci ana jiran faruwar haka

https://p.dw.com/p/1FyWh
Nigeria Poster von Präsident Mohammadu Buhari vor Militär
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

To sun dai gaji aikin jagorancin rundunonin sojan Najeriyar a dai dai lokaci da aikin nasu ke fuskantar kalubalen da bai taba shiga irinsa a tarihin Najeriyar ba, domin kuwa duk da nasarar da sojojin ke ganin sun samu na karbe garuruwan da 'ya'yan kungiyar Boko Haram ta kame a baya, babu sauki a fanin kai hare-hare da kusan kullumn ke dalilin aikawa da jama’a lahira.

A baya dai kokarin samun hadin kai daga kasashen makwabta irin na Kamaru, Chadi da Jamhuriyar Nijar, wadanda suma matsalar ta Boko Haram ta yi masu naso ya kasance babbar matsala da kalubale ga sojojin Najeriyar. Ko a yanzu zata iya canza zani tunda an yi sabon zubi, kuma ma daya daga cikin watau babban hafsan sojojin kasa na Najeriyar Manjo Janar Buratai ya kasance wanda ya yi mu'amala da sojojin kasashen a matsayinsa na kwamandan rundunar kasa da kasa da ke a Chadi? Mallam Kabiru Adamu kwararre ne a kan harkokin tsaro a kasashen Afrika ta yamma.

"ka ga shi Janar Burutai ya je Njamena ya zauna a Chadi da ma sauran sojojin kasashen an yi mahganganu na fili da ma sirri wadnda ni da kai bamu sani ba, to ina sa ran saboda wadnnan dalilan ba za’a samu wannan matsalar ba. Kuma in dai jagoranci ne suke bukata ai shugaban Najeriya ya nuna masu jagoranci ya samar musu da dama. Abu daya, kada su ji shakku su fitowa lamarin bisa gaskiya, wanda ya yi a yi mishi ko hukunci soja ko na zuwa kotu, don wannan zai zama gargadi ga na baya don kada suma su aikata".

Nigeria Soldaten
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A yayin da ‘yan Najeriya da dama ke hasashen sauyin da wadannan nade-nade ka iya samarwa musamman saboda kosawar da aka yin a ganin shugaba Buhari ya motsa, musamman saboda sukurkucewar da halin yanayi tsaro ya yi. Ga kungiyoyin da ke kare hakokin jama’a na cike da fatan wannan zai samar da sauyi a kan batun taken hakin jama’a da aka dade da zargin sojojin da aikatawa. Mallam Awwal Musa Rafsanjani shine shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakin jama’a na Afrika ta yamma.

" A kwai kungiyoyi da dama a cikin gida da na kasashen waje wadanda suka yi koke-koke yadda ake take hakkin jama’a ake fyade da kwace, alhali wadnda ke wannan ta’adancin an kyalle suna cin karensu ba babbaka, ga fararen hula da basu jib a basu gani ba, amma muna ganin cewa wadannan sabbin shugabanin da aka nada ba zasu maimaita irin wannan ganganci da aka yi a baya ba, don duniya zata sa masu ido kuma ‘yan Najeriya zasu sa masu ido , shi kansa shugaban kasa ba zai yadda mutuncinsa a zubar mashi da shi ba’’.