Harin ta'addanci a birnin Tel Aviv
June 9, 2016Talla
'Yan bindigar Palasdinawa guda biyu ɗauke da bindigogi sun buɗe wuta ne daf da lokacin da jama'a ke kai da kawo tare da iyalensu a cikin gidajen na sayer da abinci.Maharan waɗanda 'yan sanda suka gano cewar mazauna wasu ƙauyukan Yankin gabar Gokin Jordan ne tuni da aka cafkesu.
Firaministan na Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda ya dawo daga wata ziyara daga Rasha ya yi Allah wadai da harin.
''Wannan wani hari ne na dabanci da 'yan ta'addar suka kawo a tsakiyar birnin Tel Aviv a kan farar hula waɗanda ba su san hawa ba balantana sauka ba.