1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Martani bayan hari a dajin Koure

Salissou Boukari LMJ
August 10, 2020

A Jamhuriyar Nijar kwana guda bayan wani harın ta'addanci da ya halaka mutane takwas shida 'yan kasar Faransa biyu 'yan Nijar, jama'a da masu sharhi kan harkokin tsaro na yin tsokaci kan yanayin da aka kai harin.

https://p.dw.com/p/3gid5
Niger Französische Touristen getötet
MAsu yawon bude idanu daga Faransa da 'yan rakiyarsu sun halaka yayin hari a NijarHoto: AFP

Faransawan shida dai na aiki ne da wata kungiya mai zaman kanta yayin da mutanen biyu 'yan Nijar suka hadar da direban da ke dauke da su da kuma shugaban kungiyar masu yi wa 'yan yawon buda idon jagoranci a dajin Koure, inda aka kai harin.

Babban abun da ya fi daukar hakanli dai cikin wannan lamari, shi ne ganin matsayin dajin na Koure inda aka kai wannan hari ga kasar ta Nijar. A dajin ne dai ake da rakuman daji da ake ganin sune suka yi saura a yammacin Afirka kuma wuri ne da lokaci zuwa lokaci masu yawon buda ido na cikin gida da ma kasashen waje, ke zuwa domin kallo ganin cewa ba shi da nisa da Yamai babban birnin kasar ta Nijar.
Tuni dai ake ganin su kansu wadannan masu zuwa yawon buda ido sun yi kasada, ganin cewa kasashensu da ma kasar Nijar na yin jan hankali ga duk bakin da ke da niyar shiga irin wadannan dazuka domin kuwa ba a sanin inda mugu yake ba. Ga masu sharhi kan harkokin tsaro kamart Alkassoum Abdourahamane wannan hari ya sa dole a aza ayar tambaya.

Niger Giraffen aus dem Kouré Giraffe Reserve
A dajin Kouré na Jamhuriyar Nijar ne ake da ragowar Rakumin dawa a Afirka ta YammaHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Wata majiya da wata jarida ta rawaito dai, ta sanar da cewa jami'an tsaro sun cafke daya daga cikin maharan yayin da suke ci gaba da neman sauran. Sai dai a cewar gwamnan jihar Tillabery Tidjani Kacalla jihar da wannan hari ya afku, maharan dai a kullu yaumin sauya salo suke kuma ita ma gwamnati na tsaye tsayin daka.

Tuni dai wasu masu hangen nesa suka soma nazarin yadda za ta kaya a nan gaba, ganin yadda kasar ta Nijar ke kara karkata sannu a hankali ga shirye-shiryen zabukan gama gari da za a soma da na kananan hukumomi a ranar 13 ga watan Disambar wannan shekarar da muke ciki, inda ake ganin ya kyautu tun yanzu a yi wa tubka hanci.