Harin kunar bakin wake aka kai Rasha
April 4, 2017Talla
Masu bincike a kasar Rasha suna zargin dan kunar bakin wake dan shekaru 22 daga kasar Kyrgyzstan kan harin bam a jirgin karkashin kasa na St. Petersburg birni na biyu mafi girma a kasar. Hukumomin Rasha sun kara kaimin bincike neman bankado wadanda ke da hannu a cikin harin da ya hallaka mutane 14 yayin da wasu kusan 50 suka samu raunika.
An kai harin lokacin da Shugaba Vladimir Putin yake ziyara a birnin na St. Petersburg inda yake ganawa da Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus. Kasashen duniya da dama sun fito fili sun yi tir da halin yayin da manyan kasashe ke cewa za su taimaka cikin binciken da ake yi na neman wadanda suke da hannu a harin na Rasha.