1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin gurneti gaban majalisar dokoki a Ukraine

Yusuf BalaAugust 31, 2015

Harin dai na zuwa ne bayan wata zanga-zangar kishin kasa a gaban ginin majalisar dokokin kasar da ke birnin Kiev, inda masu adawar suke sukar shirin wata doka kan 'yan aware.

https://p.dw.com/p/1GOaf
Ukraine Kiew Auseinandersetzungen an der Werchowna Rada
Masu zanga-zanga a KievHoto: picture-alliance/dpa

'Yan sanda da dama da wasu jami'ai masu damara na kasar Ukraine sun sami raunika bayan kai wani hari da makaman gurneti da aka kai ga wani dandazo na masu zanga-zangar kishin kasa a gaban ginin majalisar dokokin kasar da ke birnin Kiev, inda suke adawa da shirin wata doka da za ta ba wa yankin 'yan aware wani iko na musamman kamar yadda 'yan sandan suka bayyana.

A cewar wani dan jarida da ke daukar wa kamfanin dillancin labaran Reuters TV hoto ya ce da dama cikin 'yan sandan sun sami raunika a kafa, inda wurin da aka yi zanga-zangar kuma jini ya watsu a ko'ina.