1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya hallaka mutane a Kaduna

April 8, 2012

Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu a wani harin ta'addanci a garin Kaduna dake arewacin Najeriya. Babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin harin.

https://p.dw.com/p/14ZZm
epa03026909 Nigerian police control a street shortly after a bomb blast in a market in Ogbomoshoin area of Kaduna, Nigeria, 07 December 2011. Reports state the early morning explosion in the northern city of Kaduna killed 10 people, including a pregnant woman and two children. A group suspected to be Islamist militants reportedly arrived on motorbikes and threw bombs into the crowded spare parts market. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A Najeriya mutane da dama ne suka rasu yayin da wata mota maƙare da bama bamai ta yi bindiga a cikin garin Kaduna dake arewacin Najeriyar. Kakakin hukumar agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Yushau Shuaibu yace an sami mutane da dama waɗanda suka jikata, an kuma garzaya da su zuwa asibitoci domin yi musu magani. Sai dai bai bada adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, inda yace suna cigaba da tattara bayanai.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya fito ya baiyana ɗaukar alhakin harin. Wani wanda ya ganewa idanunsa aukuwar lamarin yace yawancin waɗanda suka rasu da kuma waɗanda suka jikata 'yan Achaba ne da direbobin taxi da kuma almajirai. Jakadun ƙasashen waje da hukumomin tsaron Najeriya tun farko sun yi gargaɗi da cewa kungiyar Boko Haram ka iya kai hari a lokaci bukukuwan Easter.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe