1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a kan asibitin soji a Kabul

Zainab Mohammed Abubakar
November 2, 2021

Kusan mutane 20 ne suka rasa rayukansu daura wasu sama da 50 da suka jikkata a wasu hare hare da aka kai a asibitin sojoji mafi girma a birnin Kabul na kasar Afghanistan.

https://p.dw.com/p/42Tak
Afghanistan Kabul | Anschlag auf Vize-Präsident Amrullah Saleh
Hoto: Rahmat GulAP/picture alliance

Rahotanni na nuni da cewar wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da abubuwan fashewa da ke jikinsa a kofar shiga katafaren asibitin Sardar Mohammed Daud Khan mai gadajen jinya 400 da ke tsakiyar Kabul, daga nan kuma sai wasu 'yan bindiga suka fara buda wuta a cikin asibitin, a cewar gwamnatin Taliban.

Kakakin ma'aikatar lafiya ya sanar da cewar, an samu gawarwakin mutane 19, a yayin da aka yi jigilar sama da mutum 50 zuwa asibiti.

Harin na wannanTalatar dai, shi ne na baya bayannan a Afghanistan din tun bayan da 'yan Taliban suka kwace mulkin wannan kasa da yaki ya daidaita.