1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata da yara sun halaka a wani hari a Yemen

Gazali Abdou Tasawa
September 24, 2019

Mutane 16 da suka hada da kananan yara sun halaka a cikin wasu hare-hare ta sama a garin Qohtoba na kasar Yemen da ke hannun 'yan tawayen Huthi.

https://p.dw.com/p/3QA4g
Jemen Luftangriff auf Hodeidah
Hoto: Reuters/A. Zeyad

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa mutane 16 da suka hada da kananan yara bakwai da mata hudu sun halaka a cikin wasu tagwayen hare-hare ta sama da aka kai a wanann Talata a garin Qohtoba na Jihar Daleh na kudancin Yemen da ke a hannun 'yan tawayen Huthi.

 Hukumomin kiwon lafiya na birnin na Qohtoba sun ce illahirin iyalan gida daya ne suka halaka a cikin harin na farko, a yayin da sauran wadanda suka halakan jami'an ceto ne wadanda harin na biyu ya ritsa da su a daidai lokacin da suka zo kawo dauki ga wadanda harin farko ya ritsa da su.

 Tashar Talabijin ta Al-Massirah mallakar 'yan tawayen na Huthis ta dora alhakin kai wannan hari ga rundunar kawancen kasashen Larabawa da ke yaki a kasar Yemen a karkashin jagorancin Saudiyya.