1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Saudiyya ta kashe 'yan Yemen

Mouhamadou Awal Balarabe
December 19, 2017

Akalla fararen hula 136 sun rasa rayukansu a Yemen a cikin kwanaki goma da Saudiyya da kawayenta suka yi amfani da su wajen rubanya hare-hare ta sama a a kasar, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/2pdl4
Houthis tragen die Leiche eines Mannes, der durch Luftangriffe in ein von Houthi geführtes Haftzentrum in Sanaa getötet wurde
Hoto: Reuters/K.Abdullah

A lokacin da yake wa manaima labarai bayani a birnin Geneva, kakakin hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Rupert Colville ya nuna damuwa da sumamen sojojin kawance ke kai wa kan 'yan tawayen Huthi inda aka kashe mutane 136. Daga cikin wuraren da sumamen suka fi barna har da gidan yarin Sana'a inda mutane 45 suka mutu.

Tun dai shekaru biyun da suka gabata ne Saudiyya ta shiga ciin rikicin da Yemen da ke fama da shi da nufin fatattakar 'yan shi'an Huthi da ke suka karbe iko da Sana'a babban birni. Sai dai kuma fadan ya gazance bayan da Huthi suka kashe tsohon shugaba Ali Abdallah Saleh sakamakon saba yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

Mutane 8 750 suka rigamu gidan gaskiya a tsukin wadannan shekaru a Yemen yayin da dubbai kuma suka jikata.