1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haraji akan hada hadar bankunan Turai

October 7, 2010

Tarayyar Turai ta amince da sabon shirin sanyxa haraji akan ribar da bankunan nahiyar ke samu.

https://p.dw.com/p/PYr9
Babban bankin TuraiHoto: DW

Hukumar tarayyar Turai ta goyi bayan bullo da haraji daban daban akan ribar da bankuna ke samu da kuma irin kudadden alawus alawus da ake baiwa ma'aikatan bankunan. Shugabannin hukumar tarayyar Turai suka ce ba'a sanyawa bankuna harajin daya kamata su rinka biya, kana suka ce al'amuran da suka shafi tu'ammuli da kudade ka iya janyo harajin daya kai na zunzurutun kudi euro miliyan dubu 25 a duk shekara, wanda za'a iya yin amfani da shi wajen tallafawa tattalin arzikin kasashen da suka fuskanci matsalar kariyar tattalin arziki.

Sai dai kuma hukumar tarayar Turai din ta yi watsi da kokarin da kasashen Jamus da Faransa da kuma Austria suka yi na neman a sanya haraji akan hada hadar hannun jarin da bankuna suka gudanar, inda shugabannin tarayyar Turai suka ce hakan zai kasance mai alfanu ne kawai idan har daukacin kasashen duniya ne za su aiwatar da tsarin, domin a cewar su masu zuba jari na da zabin garzayawa zuwa kasashen da ba sa yin aiki da tsarin. Wannan dai yana nufin kasar Birtaniya za ta iya yin asarar wasu harkokin kasuwancin ta idan ana bin wannan sabon shirin.

Shugabannin tarayyar Turai dake birnin Brussels sun bayyana shirin gabatar da bukatar samar da tsarin sanya haraji akan hada hadar hannun jari a lokacin taron kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya ta G20, wanda zai gudana cikin watan Nuwamba - idan Allah ya kaimu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal