1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hanyar neman inganta Tafkin Chadi

February 28, 2018

Hanyar ceto Tafkin Chadi daga barazana ta kafewa shugabanni na kasashen yankin game da kwararru sun share lokaci suna nazarin mafitar matsalar da ta yi sanadiyar tashin hankali da annoba na  ta’addanci.

https://p.dw.com/p/2tTsH
Afrika - Tschadsee
Hoto: Getty Images/AFP/S. K. Kambou

A cikin kankanin lokaci ne dai daukacin yankin Tafkin Chadin ya dauki hankalin duniya sakamakon rigingimu na ta’addancin da nau’o’in tayar da hankalin da ke zaman ruwan dare a cikin yankin yanzu. Kuma janyewar tafkin daga fadin muraba’in Kilo-mita 25000 ya zuwa kasa da kashi 10 cikin 100 na fadin ne dai ake yi wa kallon ummul’aba’isin rikicin da ke barazana ga mutane kusan milyan 40 a daukacin yankin tafkin.

Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Harnik

Shugabanni biyar daga Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Najeriya da Chadi da Afirka ta Tsakiya suka hallarci taron ko bayan wakilai daga Majalisar Dinka Duniya da manyan bankunan raya kasa na duniyar da sauran masu ruwa da tsaki da makomar yankin ke hankoron mafita a cikin yankin mai tasiri a fadar Shugaba Mouhamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar kuma shugaban hukumar gudanawar tafkin Chadi.

Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Sake farfado da tafkin dai na iya kai ga rage yawan ‘yan ciranin da ke tururwa na zuwa kasashen Turai da sojan hayar da suka mamaye daukacin tsakiyar nahiyar Afirka. Ko bayan samar da aiyyukan yi a tsakanin milyoyi na mutanen yankin.