Hana masu mulkin kama karya barci
September 22, 2020Manufarmu: Bayanai masu inganci
A sassa dabam-dabam na duniya, dimukuradiyya na ci gaba da fuskantar kalubale, daura da matsalar hana 'yancin fadin albarkacin baki. A kasashen da kafofin yada labarai ke hannun masu mulki, ana tilasta mutane zabar abin da ba sa so. Dalili ke nan da ya sa muka dukufa wajen samar da bayanai ba tare da son zuciya ba, da daraja 'yancin fadin albarkacin baki da tsarin dimukuradiyya a kasashe sama da 180. Ta hana masu mulkin kama karya su rintsa idanunsu.
Yadda muke taimaka wa 'yancin fadin albarkacin baki
DW na kokarin dauko labarai masu sarkakiya da suka shafi 'yancin fadin albarkacin baki, ta hanyar karin haske kan rigingimu da wadanda ake take 'yancinsu. Shirin da ke mahawara don taimakawa halin da suke ciki. Rahotannin da suka kunshi hira da masu fafutuka da fitattu a fannin ilimi da jarumai da masu zanen barkwanci da marubuta daga bangarori dabam-dabam na duniya. A kullum idanunmu na kan batutuwan da ke taimaka wa 'yancin fadin albarkacin baki da walwala.
Tun daga shekara ta 2015, DW ke karrama wadanda suke taka rawa a fafutukar 'yancin fadin albarkacin baki da kyautar musamman mai taken: DW Freedom of Speech Award. Masu cin gajiyar wannan kyautar sun hadar da marubuta a kafar internet wato (Bloggers) da aka jefa a kurkuku da 'yan jaridar da ke jajircewa a aikinsu da kuma mutanen da ke fafutukar tabbatar da 'yancin kafofin yada labaran.
Muhawara kan nuna bambanci
An samu sauyi sosai a tafiyar da ayyukan kafofin yada labarai a shekarun baya-bayan nan. Ba kawai tsakanin matasa kadai ba, amma har da sassa dabam-dabam na rayuwar dan Adam. Fasahar zamani da shafukan sada zumunta, sun taimaka wajen samun muhawara tsakanin rukuni dabam-dabam na al'umma.
Ja'afar Talk, wani shiri ne na muhawara da ke bai wa mutane damar tofa albarkacin bakinsu kan yadda lamura ke tafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman batutuwan da sauran kafofin yada labarai ba sa iya magana a kai.
Bisa la’akari da matasa a matsayin wadanda suka fi yawa a cikin al'ummar Afirka, tashar DW na ba su damar bayar da tasu gudunmowa a shiri na musamman da ta kirkira mai taken: "Matasa Kashi 77 ne," wanda karkashinsa ake bai wa matasan damar yin muhawara da ake kira da "The 77 Percent - Street Debate" cikin harshen Ingilishi. Shiri ne na muhawara a kan titi tsakanin matasan nahiyar masu kwazo da basira da hazaka, wanda ke ba su damar tattauna batutuwan da suka shafi rayuwarsu. Sashen Hausa na DW a hannun guda, kan bai wa matasan damar yin tsokaci ko ba da gudunmawa ta shirinmu na "Ra'ayin matasa," ta shafukanmu na sada zumunta na Facebook da Instagram daYouTube.
Bugu da kari, sashen Hausa na DW na bai wa mutane damar yin muhawara kan muhimman batutuwa na rayuwa da ake gabatarwa ta rediyo kamar zauren "Ra'ayin Malamai" da kuma shirin "Darasin Rayuwa," inda mutane kan fadi ra'ayoyinsu da labaran da suka shafi rayuwarsu.
Kallon batutuwan kamar yadda suke
Shin 'yan kasar Lebanon na da 'yancin bayyana ra'ayoyinsu a shafukan internet fiye da al'ummar kasar Ghana? Makarantar horar da 'yan jarida wato DW Akademie, kan bayar da damar amfani da fasahar zamani ta #speakup barometer wajen cimma 'yancin fadin albarkacin baki da bayanai, a zababbun kasashe da take aiki domin inganta ci-gaban kafofin yada labarai, tare da hadin gwiwar abokan huldarta.
Karin Bayani: Media Freedom Navigator
Aikin jarida na ci gaba da fuskantar kalubale a Turkiyya. Dangane da haka ne tashar DW da hadin gwiwar BBC da France 24 da Muryar Amirka, suka samar da kafar YouTube +90, domin bai wa Turkawa damar samun sahihan bayanai da za su taimaka musu. Ana iya samun kafar ta YouTube ta hanyar amfani da wannan lambar +90, da ake sakawa bayan lambobin buga waya zuwa ketare daga Turkiyya.
Isar da sakonni
Saboda ci-gaba na fasahar zamani, mutane na iya samun bayanai cikin sauki. Sai dai har yanzu akwai kasashen da ake ci gaba da toshe hanyoyi na samun bayanai ko labarai, musamman ta kafar internet. Dangane da haka ne DW ta mayar da hankali wajen yakar wannan dabi'a ta toshe kafar samun bayanai daga al’umma. Ana iya samun labaran DW tare da tallafin wasu hanyoyi na internet guda biyu wato: OIF (Open Technology Fund) da kuma TorProject (The Onion Routing). A sauwake za ka kama tashar DW da kuma sauran kafofin yada labarai kamar New York Times da BBC da makamantansu.
Karin Bayani: Bypasscensorship.org