1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dauki matakin karfafa tsaro a Singapor

Ramatu Garba Baba
June 6, 2018

An dauki mataki na dakatar da jiragen sama daga wucewa a sararin samaniyan kasar Singapor a yayin zaman ganawar shugaba Donald Trump na Amirka da takwaransa na Koriya Ta Arewa Kim Jong-Un.

https://p.dw.com/p/2yzwt
USA Nordkorea - Donald Trump und Kim Jong Un - TV
Hoto: picture alliance/AP Photo/L. Jin-man

Hukumar kula da lafiyar jiragen sama ta kasa da kasa ICAO ce ta sanar da daukar matakin a wannan Laraba. Za'a a soma dakatar da jiragen a yayin da kasar za ta karbi bakuncin shugabanin biyu tun daga ranar goma sha daya zuwa goma sha uku na wannan watan Yunin saboda dalilai na tsaro acewar hukumar.

Shugabanin biyu sun dadde suna musayar zafafan kalamai a tsakaninsu bisa batun nukiliyar Koriya ta Arewa amman ana ganin wannan zama mai cike da dinbin tarihi ka iya zama silar warware wannan takaddama da ma fatan ganin Koriya ta Arewan ta amince da kawo karshen shirin nukiliyarta baki daya.