1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta yi barazanar kai hari kan Isra'ila

April 30, 2022

Kungiyar Hamas ta yi gargadin kaddamar da hare-hare a wuraren ibadun Yahudawa idan har Isra'ila ta ci gaba da kai sumame masallacin Al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudus.

https://p.dw.com/p/4AfJV
'Yan kungiyar Hamas a Zirin Gaza
Hoto: Yousef Mohammed/IMAGESLIVE via ZUMA Press/picture alliance

Shugaban kungiyar ta Hamas da ke zirin Gaza Yahya Sinwar ya ce kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen lalata dubban wuraren ibadun Yahudawa a fadin duniya, muddin aka ci gaba da dauki ba dadi a masallacin Al-Aqsa.

A makwannin baya-bayan nan dai takaddama ta yi ta barkewa tsakanin Falasdinawa da jami'an 'yan sandan Isra'ila a harabar masallacin, lamarin da kasashen Musulmai ke tir da yadda jami'an ke harba hayaki mai sa hawaye kan Falasdinawan.

Idan har ba a kawo karshen takaddamar ba, kungiyar Hamas dai ta yi barazanar harba rokoki kan Isra'ila a karshen watan Mayun wannan shekarar, a lokacin da Israila ke bikin tunawa da mamaye birnin na Kudus.

Rikicin na baya-bayan nan na haifar da fargabar sake barkewar mummunan rikici makamancin na shekarar bara da aka kwashe tsawon kwanaki 11 ana gwabza yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar ta Hamas.