Hamas ta saki wasu Amurkawa da ta tsare
October 21, 2023Talla
Offishin firanministan Isra'ila ne ya tabbatar da sakin Judith da kuma Natalie Raanan. Tuni dai Shugaba Joe Biden na Amirka ya nuna fari cikinsa kan samun 'yancin mutanen. Alkalumman gwamnatin Isra'ila sun yi nuni da cewa, kimanin mutane 200 ne kungiyar ta Hamas ke tsare da su a zirin Gaza.
Karin bayani: Kasashe na tir da sabon rikicin Isra'ila da Hamas
A share guda, ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Bearbock na ziyara a Isra'ila domin nuna goyon baya ga gwamnatin kasar. Ministar na kuma ziyarar ce da nufin taimakawa Falasdinawa su samu damar samun kayan agaji.