Hamas ta nemi a fita intifada ranar Juma'a
December 7, 2017Talla
An dai shiga zanga-zanga a yankin Falasdinawa bayan da Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila. Shugaban kasar Turkiya Tayyip Erdogan da Fafaroma Francis sun amince a wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan rana ta Alhamis cewa duk wani kokari na sauya matsayar Birnin Kudus abu ne da ya kamata a kauce masa kamar yadda ofishin Erdogan ya bayyana.
A cewar majiyar labarin dukkanin shugabannin biyu Erdogan da Fafaroma sun amince cewa birnin Kudus waje na ibada mai tsarki ne da mabiyan addinin Musulinci da Kirista da ma mabiya na addinin Yahudu. Tuni dai kungiyar Hamas ta sha alwashi na fita intifada a karo na uku a ranar Juma'a abin da ke haifar da fargabar kwarara ta jini da rasa rayuka.