Hamas ta amince da tayin tsagaita wuta a Gaza
May 6, 2024Masu aiko da rahotanni daga yankin sun ce jim kadan bayan sanar da wannan mataki da aka dade ana jira jama'a sun fantsama kan titunan birnin Rafah inda suka yi ta raye-raye na nuna murna har ma da harba bindiga a sarararin samaniya.
Karin bayani: Biden: Fata kan tsagaita wuta a Gaza
Wani jigo a kungiyar ta Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa yanzu zabi ya rage ga Isra'ila bayan da kungiyar ta bayyana cewa ta amince da tayin sulhun da kasashen Qatar da Masar da ke kai komo wajen shiga tsakani a rikicin Gaza suka gabatar mata.
Karin bayani: Isra'ila da Hamas za su sake hawa kan teburin sulhu
Sai dai jim kadan bayan fidda wannan sanarwa, an ambato wani jigo a gwamnatin Isra'ila na cewa ba za su lamince da wasu tanade-tanade da daftarin yarjejeniyar ta kunsa ba.