1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan takarar Hama Amadou a Nijar

Mahaman Kanta / LMJSeptember 14, 2015

Al'ummar Nijar na ci gaba da mayar da martani kan tsayar da Hama Amadou da Jam'iyyarsa ta Moden Lumana Africa ta yi a matsayin dan takarta a zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1GWIg
Hama Amadou dan takara a jam'iyyar Lumana ta Nijar
Hama Amadou dan takara a jam'iyyar Lumana ta NijarHoto: DW/S. Boukari

Jam'iyyar ta Moden Lumana Africa ta bayyana Hama Amadou da a yanzu haka yake gudun hijira a kasashen ketare, a matsayin wanda zai tsaya mata takara a kujerar shugabancin kasar da za a gudanar a shekara ta 2016 mai zuwa ne yayin taronta da ta gudanar a karshen mako. Karo na biyu ke nan dai jam'iyyar ta Lumana na kaddamar da Hama a matsayin dan takararta a zaben shugabancin kasar, duk kuwa da yake a yanzu yana matsayin dan gudun hijira. Kungiyoyin farar hula dai da ke fafutukar tabbatar da dimokaradiyya a Nijar din sun ce a ganinsu babu wani aibu a tsayar da Hama Amadou a matsayin dan takara duk kuwa da cewa baya kasar. Maina Karte masani ne a kan harkokin shari'a a Jamhuriyar ta Nijar ya kuma ce ba tilas bane sai Hama ya kasance a kasar kafin ya samu damar tsayawa takarar. A cewarsa a wasu kasashen kundin tsarin mulkin kasar ya nunar da cewa tilas ne sai dan takara ya kasance dan kasa kana yana cikin kasar tsahon watanni shida kafin a tsayar da shi takara, sai dai abin ba haka yake ba a Jamhuriyar Nijar, a dangane da haka takarar Hama ba ta saba dokokin kasar ba. Hama Amadou dai ya kasance tsohon kakakin majalisar dokokin Jamhuriyar ta Nijar kafin ya tsere zuwa gudu´n hijira bisa tuhumarsa da hannu a badakalar cininkin jarirai.