HALIN DA AKE CIKI A KASAR TOGO.
February 11, 2005To a yanzu haka babban abinda yafi daukar hankali a nahiyar ta Africa musanmamnma a kasar ta Togo shine na yadda shugaban kungiyyar hadin kann nahiyar wato Shugaba Obasanjo ya soke ziyarar daya shirya kaiwa izuwa kasar ta togo don warware matsalar rikicin da kasar ta fuskanta bayan rasuwar Shugaba Eyadema.
A dai can baya an shirya cewa Obasanjon zai iasa kasar ta Togo a yau juma a don saduwa da sauran shugabannin kasashe a nahiyar dake cikin kungiyyar Ecowas don tattauna hanyoyin warware rikicin siyasar kasar.
Daukar wan nan mataki a cewar mai magana da fadar gwamnatin ta Nigeria wato Remi Oyo ya biyo bayan hana jirgin daya dauko tawagar shugaba Obasanjo sauka ne a filin jirgin saman kasar na Togo,bisa irin matakin da shugaban na Nigeria yace kungiyyar Au zata dauka a kann sabuwar gwamnatin kaar muddin ba a koma tafarkin kundin tsarin mulkin kasar ba wajen nadin sabon shugaban kasar ta Togo.
Remi Oyo tace mahukuntan na Togo sun hana saukar jirgin daya kwaso tawagar ta Obasanjo ne a daren jiya alhamis a kokarin da suke na kawo cikis game da niyyar kungiyyar Au da Ecowas na warware rikicin siyasa da kasar ta fada a ciki sakamakon rasuwar shugaba Eyadema da yafi kowa ne shugaba dadewa a kann karagar mulki a nahiyar ta Africa.
A kuwa ta bakin ministan cikin gida na kasar ta Lome, Francois Boko ya shaidar da cewa kafin jirgin tawagar Obasanjo ya taso sun umarci daya dakata tukuna domin an canja gurin da za a gudanar da wan nan taron sulhu,amma tawagar tayi shakulatin bangaro dashi,wanda bisa hakan ne a cewar ministan gwamnatin ta Togo ta dauki wan nan mataki.
A daya hannun kuma Remo Oyo taci gaba da cewa bisa wan nan mataki da mahukuntan na Togo suka dauka a yanzu haka gwamnatin ta Nigeria ta bukaci jakadan kasar ta a lome ya dawo gida.
Jim kadan dai bayan sanarwar da kasar ta Togo ta bayar na nadin Faure Gnassingbe a matsayin sabon shugaban kasar bayan rasuwar mahaifin sa,kungiyyar ta Au da kuma ta tattalin arzikin kasashen yammacin Africa wato Ecowas tayi Allah wadai da wan nan mataki tare da barazanar kakabawa kasar takunkumi matukar bata dawo daga rakiyar wan nan mataki data dauka ba.
Faure dake da shekaru 38 ya samu darewa wan nan kujera mai mai alfarma ne ta kasar ta Togo bayan rundunar sojojin kasar sun mara masa baya na darewa wan nan mulki.
A dai kundin tsarin mulkin na Togo shugaban majalisar dokokin kasar ne yakama ya dare wan nan mukami ba wai wani mutum na daban ba,kamar yadda hakan ya faru na nadin dan shugaba Eyadema a wan nan matsayi.
A wata sabuwa kuma a a yau juma jamian yan sanda a kasar ta Togo sun harba barkokon tsohuwa a cikin gungun mutane dake gudanar da zanga zangar nuna rashin amanna game da wan nan mataki da sojojin kasar suka dauka da cewa bai dace ba ko kadan.
Rahotanni dai daga kasar a can baya na nuni da cewa da yawa daga cikin jamiyyun adawar kasar na cike da zaton cewa bayan rasuwar Shugaba Eyadema za a samu damar bude sabon babin ci gaba a kasar ta togo na gudanar da cikakken mulkin dimokradiyya,amma da alama wan nan fata a yanzu haka na neman komawa ciki.
Ibrahim Sani.