1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya za ta sa ido kan Saudiyya

Salissou Boukari MNA
November 5, 2018

A wannan Litinin kwamitin kare hakin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama domin duba batun take 'yancin dan Adam a kasar Saudiyya biyo bayan mutuwar Jamal Khashoggi.

https://p.dw.com/p/37edT
Schweiz Michelle Bachelet bei der Welthandelsorganisation in Genf
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Trezzini

Hakan na zuwa ne bayan guguwar da ta taso sakamakon batan dabo da dan jaridar nan na kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi ya yi, wanda kuma ake zargin hukumomin na Saudiyya da hallaka shi a karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya.

Duk bayan shekaru hudu ne dai kwamtin kula da kare hakin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ke irin wannan zama domin duba inda aka fi samun matsalolin take hakin bil Adama.

Saudiyya dai na cikin tsaka mai wuya inda take shan suka tun bayan mutuwar dan jaridar.

A yanzu haka Amirka na ci gaba da matsa mata kaimi na ganin ta dakatar da kai hare-haren da take yi a kasar Yemen.

Daga nata bangare kasar Birtaniya ta yi kira ga abokan huldarta da ke cikin Kwamitin Sulhu da su dauki matakai kan kasar ta Saudiyya dangane da yakin da take yi a kasar ta Yemen domin ganin an warware rikicikin ta hanyar siyasa.