Hafsan sojin Aljeriya Gaid Salah ya rasu
December 23, 2019Talla
Janar Gaid Salah wanda ya rasu yana da shekaru 79, ya kasance jigo a harkokin mulkin kasar ta Aljeriya tun daga shekara ta 1962, sannan ya taka muhimmiyar rawa wajen tilasta wa Shugaba Abdelaziz Bouteflika yin murabus a watan Aprilun da ya gabata a bisa matsin lambar masu zanga-zangar neman sauyi.
Marigayi Janar Gaid Salah ya kuma kasance a sahun gaba na hukumar mulkin sojan da ta jagorancin kasar har ya zuwa zaben sabon shugaban kasa na ranar 12 ga wannan wata na Disemba wanda Abdelmajid Tebboune ya lashe.
Tuni dai sabon shugaban kasar ta Aljeriya ya kaddamar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar tare da nada Janar Said Chengriha mataimakin shugaban hafsan sojan kasar a matsayin sabon shugaban hafsan soja na wucin gadi na kasar.