Hadin gwiwa don kawo karshen masu tsattsauran ra'ayi
September 25, 2014Baki dayan mambobin kwamitin 15 sun amince da sababbin matakan yayin wani taro na musamman da suka gudanar, inda suka ce ya zamo wajibi ga baki dayan kasashen da suka kasance mambobi a Majalisar Dinkin Duniya 193, su dakile yaduwar kungioyoyin masu kaifin kishin addini irin su IS da yanzu haka ke neman zama barazana ga tsaron duniya baki daya. A jawabinsa yayin taron da ya jagoranta, shugaban Amirka Barack Obama ya ce akallah masu kaifin kishin addini 15,000 daga kasashe 80 aka hakikance sun tafi Siriya a 'yan shekarun nan domin yin abun da suke kira da jihadi. Bayan kammala taron na Kwamitin tsaro ma'aikatar harkokin tsaro ta Amirka ta sanar da kaddamar da sababbbin hare-hare a kan kungiyar IS a Siriya. A wani labarin kuma shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya Rami Abdulrahman ya ruwaito cewa akallah mayakan IS 14 da fararen hulabiyar ne suka hallaka sakamakon hare-haren da Amirka da kawayenta ke kaiwa a yankunan da 'yan IS din suke a kasar Siriyan.