1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai harin bam kan babban birnin Tigray

November 16, 2020

Kwamitin Nobel da ya bai wa Abiy Ahmed lambar yabo ta zaman lafiya a 2019 ya nuna damuwa game rikicin da kasar ke ciki tare da yin kira kan sassauta lamarin.

https://p.dw.com/p/3lNSE
Äthiopien Amhara-Soldaten auf dem Weg nach Tigray
Hoto: Tiksa Negeri/REUTERS

Rundunar gwamnatin Habasha ta kai wani hari bam ta sama a ciki da kewayen babban birnin Tigray a cewar wata majiya daga rundunar, rikicin da ke kara yin kamari tun makwanni biyu da suka gabata.

Yayin zantawarsu da kamfanin dillancin labarai na Reuters, sun baiyana cewa ba bu sanarwa game da wadanda suka jikkata ko lalacewar wani abu. Har yanzu dai ba bu wata sanarwa daga bangaren gwamnatin kasar, sai dai hukumomin Tigray sun ce bam ya tashi da goshin asubahin wannan Litinin.

A gefe guda kuma kwamitin Nobel da ya bai wa Firaministan Abiy Ahmed lambar yabo ta zaman lafiya a 2019 ya nuna damuwa game rikicin da kasar Habasha ke ciki tare da yin kira kan sassauta lamarin.