1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: MDD ta yi gargadi kan kamen mutane.

November 17, 2021

Alkalummar Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa daga makon da ya gabata kawo yanzu kimanin mutane 1,000 ne ake tsare da su a kasar Habasha. 

https://p.dw.com/p/435dz
Äthiopien | Verlassener Panzer nahe Mehoni
Hoto: Eduardo Soteras/AFP/Getty Images

A cikin sanarwar da majalisar ta fitar, ta ce yawancin wadanda aka kama dai sun fito ne daga yankin Tigray. An samu karuwar kama mutane a kasar tun bayan da gwamnati ta ayyana dokar ta baci ta tsawon watanni shida a farkon wannan watan yayin da ta ke fargabar mayakan TPLF na yankin Tigray ka iya kutsawa babban birnin kasar Addis Ababa.

Majalisar ta kuma ce an kama da dama ne ba tare da wani kwakwaran dalili ba kuma aka cunkushe su a wuri guda. Rikicin da aka kwashe kimanin shekara guda ana gwabzawa tsakanin dakarun Habasha da mayakan Tigray dai ya haifar da matsalar rashin samun abinci mai gina jiki a yankin Tigray. 

Ana cigaba da samun karuwar mutuwar yara saboda yunwa inda kawo yanzu kimanin yara 186 suke mutu, ake kuma hasashen ta yiwu adadin ya ninku saboda jami'an lafiya ba sa samun damar shiga yankunan da ake fama da matsalar.