Gwamnonin arewa sun gana a kan tsaro
March 3, 2021Ta'azzara da matsalar tsaro ke kara yi a Najeriya musamman a shiyyar arewa amso gabas din ne dalilin da ya sa gwamnonin suka fara gudanar da wannan taro a 'yan shekarun da suka gabata. Lura da cewa har yanzu ana ci gaba da samun koma baya a yaki da yan ta'adda, masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ya tilasta wa gwamnonin jihohin shiyyar hada karfi da karfe domin tabbatar da an samu zaman lafiya wanda sai da shi ake iya samun cigaba. Gwamnonin sun yi ikirarin cewa yunkurin nasu na dab da haifar da sakamako, a cewar shugaban gwamnonin arewa maso gabas din kuma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.
''Gano matsalolin da suke damun mu na tsaro, alama ce ta samun nasara a yakin da muke da ‘yan ta'adda. Haka ma da kokari da kwazon jami'an tsaron kasar nan wadanda suke aiki tukuru ba dare ba rana don ganin an samu zaman lafiya kasancewa tabarbarewar tsaro ya yi matukar tasiri a rayuwar al'ummar wannan shiyya. Amma a hannu guda nada sababbin shugabannin rundunonin soji da shugaban kasa ya yi, ya gwada irin kaguwar da gwamnatin tarayya ta yi wajen ganin an shawo kan matsalar la'akari da cewa kusan dukkanin shugabannin sojin suna sane da irin kalubalen da shiyyar arewa maso gabas ke ciki na lalacewar lamuran tsaro, don haka muna tsammani za a samu cigaba a kokarin da suke na tabbatar da ingantaccen tsaro a shiyyar da ma kasa baki daya''
Yayin taron dai gwamnonin sun mika bukatarsu ga gwamnatin tarayya da ta samar da sojojin haya na hadaka da wasu kasashe kan nema a irin wannan yanayi da shiyyar arewa maso gabas take ciki. Ko cikin jawabinsa gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya bukaci takwarorin nasa da su kara zage damtse wajen ganin sun cimma nasarar yakar makiya zaman lafiyar kasa.
''Karuwar ayyukan ‘yan ta'adda a wannan lokaci duk da himma da sadaukarwa ta jami'an tsaro, babban kalubale ne da kuma abin damuwa. Kamar kisan rashin imanin da aka yi wa manoma kimanin 100 a garin Zabarmari na jihar Borno a kwanakin baya da kuma yadda matsalar garkuwa da mutane ke karuwa a shiyyar musamman a jihar Taraba; da bukatar a sauya salon yaki da yan ta'ddan don kawo karshen su”
Kasancewar wannan taro shi ne irin sa na uku da gwamnonin shiyyar suka fara, ya sanya wasu daga cikin al'umma ganin ga dukkan alamu a yanzu gwamnonin sun fuskanci alkibilar da ta dace, kamar yadda masharhancin lamuran yau da kullum a jihar Bauchi Kwamaret Abdullahi Muhammad Koli ya ce.
Shi kuwa a ra'ayinsa, Malam Munkaila Ya'u, wani mai fashin baki a jihar ta Bauchi, ya ce tabbas gwamnonin sun yi abin a yaba amma kuma ya kara da cewa an bar jaki ne ana bugun taiki domin alhakin na wani fanni daban.