1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Yemen da ke gudun hijira ta sake komawa

Suleiman BabayoSeptember 16, 2015

Gwamnatin Yemen wadda take samun mafaka a kasar Saudiyya ta koma gida duk da yakin da ake a kasar.

https://p.dw.com/p/1GXQi
Zurückgetretener Jemenitischer Premierminister Khaled Bahah
Hoto: picture-alliance/dpa/Y. Arhab

Gwamnatin Yemen da ke gudun hijira ta koma gida inda Firaminista Khaled Bahah ya isa birnin Aden na kudancin kasar mai tashar jiragen ruwa a wannan Laraba. A cikin wani sakon firaministan ya ce za su tabbatar da ikon gwamnati da tsauraran tsaro, da sake gina kasa da ta lalace sakamakon yaki da 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan kasar Iran.

Firaminista Bahah da sauran mambobin gwamnati sun samu mafaka a kasar Saudiyya yayin da ake tsananin fafatawa da mayakan na 'yan tawaye, kuma firaministan ya samun rakiyar wasu ministoci da manyan jami'an gwamnatin kasar ta Yemen lokacin da ya sake komawa kasar. Sai dai kawo yanzu babu labarin lokacin da Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi zai sake komawa gida bayan tsarewa a watan Maris.