1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Turkiya ta kafa dokar ta-baci

Mahmud Yaya Azare/GATJuly 21, 2016

Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiya ya bayyana dokar ta-baci ta tsawon watanni uku a fadin kasar biyo bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi masa a makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/1JTCn
Türkei Ausnahmezustand: Folgen des Putsches
Hoto: Getty Images/C. McGrath

A wani jawabi da aka yada ta gidan talabijin na kasar, bayan wata ganawa da ya yi da manyan hafsoshin sojojin da ke ba shi shawara kan lamuran tsaro, Shugaba Erdogan ya ce, ya dauki matakin ne don kare demokoradiyya da dawo da doka da oda a fadin kasar, ba tare da keta cikakken 'yancin da 'yan kasa ke da shi ba.

Türkei - Nationaler Sicherheitsrat trifft sich unter Präsident Erdogan
Hoto: Reuters/K. Ozer

Ita dai dokar ta-baci, ta kan bai wa shugaban kasa damar yin gaban kansa ba tare da ya tuntubi majalisa ba, sannan zai iya takaita ko share duk wasu hakkoki da ake da su. Za kuma a iya amfani da dokar wajen ci gaba da tsare mutane ba tare da an gurfanar da su gaban kuliya a cikin lokacin da doka ta tanada.

Tun kafin kafa wannan dokar ta-bacin dai, alwashin da Shugaba Erdogan ya sha na kakkabe baragurbi a fadin kasar da ya kai ga tsare dubban mutane barkatai da suka haura dubu 20, da sallamar manyan jami'an gwamnati da na tsaro kimanin dubu 50, wadanda suka kunshi manyan alkalai da manyan malaman jami'a, da manyan jami'an 'yan sanda, gami da rufe dubban makarantu da kwace lasisin cibiyoyin yada labarai kimanin 50. Duk wadannan sun sanya ana ganin sanya dokar ta-bacin, a matsayin wani sabon yunkuri na yin gaban kai, don daukar fansa da wuce gona da iri kan abokanan hamayyar siyasa.

Türkei Fethullah Gülen
Hoto: picture-alliance/dpa/fgulen.com

Sai dai wasu 'yan kasar ta Turkiyya na ganin wannan mataki zai iya kaiwa ga rikidewar kasar zuwa mulkin kama karya. Zargin da babban wanda Erdogan din ke zarga da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara, Shehun Malami Fethullah Gulen ya kara nanatawa:

"Munanan hotunan da muke gani da ke nuna yadda ake cin zarafin wadanda ake tsare da su, ba ta yadda za mu yi magana kan demokiradiyya ko mutunta kundin tsarin mulki."

Turkiya dai ta nemi Amirka da ta tisa keyar shehin malami Gulen da take zargi da hannu wajen kitsa yunkurin juyin mulkin. Amirka dai ta ce tana yin nazari kan takardun shaidar da Turkiyan ta danka mata. 

Kasar Turkiya dai ta soke hukuncin kisa, amma tun bayan yunkurin juyin mulkin, Shugaba Erdogan da dama daga 'yan majalisar dokokin kasar, suka nuna aniyar dawo da dokar kisa.