1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Najeriya ta zare tallafin man fetur

January 1, 2012

Shugaba Goodluck Jonathan na shirin fuskantar ƙalubale daga ƙungiyoyin farar hula da 'yan siyasa akan matakin da gwamnatinsa ta ɗauka

https://p.dw.com/p/13cdo
Taswirar' Najeriya
Taswirar ƙasar NajeriyaHoto: AP Graphics

Gwamnatin Tarrayar Najeriya ta ba da sanarwa zare tallafin da take bayarwa akan man fetur; Sanarwa wacce hukumar tsaida farashin man fetur ɗin ta ƙasar ta baiyana, ta ce daga yau man zai koma bisa tsarin kasuwa.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka zai ƙara rura wutar rikice rikicen da ake fama da su a ƙasar. Tuni dai dama sanarwar ta haura farshin man daga Naira 65 zuwa tsakanin Naira 141 da kuma Naira 143. Abin da ya haifar da manyan layuka a wasu gidajen mai a Abuja. Sabuwar sanarwar ta kawo ƙarshen doguwar muhawarar da ta nemi raba kan al'umar ƙasar.

Duk da cewar dai sabuwar sanarwar ta tabbatar da wadatuwar man a gidaje da sauran cibiyar samun sa, daga dukkan alamu al’ummar ƙasar ta Nigeria na shiran shiga tsaka mai wuya game da bakar hajjar da suka ɗauki tsawon lokaci suna shanta cikin sauƙi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala