Gwamnati na da hannu a kisan Khashoggi
October 23, 2018A jawabinsa na farko bayan barkewar labarin kisan gillan da ya mamaye kafafen yada labaran duniya, Shugaba Erdogan ya fadawa majalisar dokokin kasar cewa, babu dayan biyu hukumomin Saudiyya ne suka tsara kisan, kuma duk wasu bayanai da gwamnatin Riyadh ta yi na dora wa wasu jami'an tsaro alhakin kisan, ba abun da duniya za ta taba gamsuwa da shi ba ne.
Don haka Erdogan ya bukaci cewa, na daya dai Sarkin Salman da ya mika mutanen 18 da ya ce wai su ke da alhakin kisan don a hukunta su a cikin kasar Turkiyya, kana na biyu ya ce akwai bukatar kafa hukumar bincike ta musamman don gano wadanda ke da hannu a kisan.
Shugaban kasar ta Turkiya, wanda bai fito a fili ya ambaci Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman ba, amma ya ce babu yadda za'a aikata kisan bada saka hannun gwamnati ba domin a cewarsa makasan sun iso Turkiya kwana guda gabanin kisan dan jarida Khashoggi, kuma an tsinke wayoyin kamarorin da ke tsaro a ofishin jakadancin da aka hallaka dan jaridan, don haka tabbas abu ne da aka dade da tsarawa.