1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamman 'yan majalisu sun fice daga APC mai mulki

Uwais Abubakar Idris GAT
July 24, 2018

Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ya dauki wani sabon salo inda sanatoci 15 da wasu 'yan majalisar wakilai 38 suka fice daga cikin jam'iyyar domin komawa jam'iyyar PDP da wasu jam'iyyun na adawa.

https://p.dw.com/p/321XB
Karikatur: Nigeria APC Streit
Rikici ya turnuke tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulkin NajeriyaHoto: DW / Abdulkareem Baba Aminu

Wannan ficewa daga APC ta wakana ce sa'o’i kalilan bayan da jami’an tsaro suka toshe gidan shugaban majalisar datawan Najeriya da mataimakinsa. Wannan mataki da sanatocin jam'iyyar ta APC da suka dauka na sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP da wasu jam'iyyun na daban na nuni da yanayin sabuwar guguwar siyasar da ke kadawa a Najeriyar inda a halin yanzu za a iya cewa da alamun kanwa ta kar tsami a ja-in-ja da aka dade ana yi da wasu 'ya'yan jamiyyar ta APC wadanda makwannin baya suka kai ga sanar da kafa bangare.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Majalisar dokokin NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Sanatocin da suka fice daga jam'iyyar ta APC sune Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi da Sanata Barnabas Gemade  na jihar Benue, Sanata Ibrahim Danbaba daga Sokoto, Sanata Shaaba Lafiaji daga jihar Kwara, Sanata Ubale Shitu na jihar Jigawa, Sanata Rafi'u Ibrahim daga Kwara, Sanata Suleiman Hunkuyi daga jihar Kaduna, Sanata Isa Misau daga Bauchi, Sanata Monsurat Sunmonu daga jihar Oyo, Sanata Soji Akanbi, Sanata Usman Nafada daga jihar Gombe, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na jihar Kano, Sanata Suleiman Nazif na jihar Bauchi, Sanata Lanre Tejuosho, Sai kuma Sanata Abdulaziz Murtala Nyako na jihar Adamawa wanda amma shi ya koma jam'iyyar ADC.

Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: picture alliance/AP Photo/S. Aghaeze

Sai dai ko baya ga wadannan 'yan majalisar dattawa 15, wasu 'yan majalisar wakilai 37 suma sun fice daga jam'iyyar ta APC a  ranar Talata, wanda ke nufin cewa a yanzu a jumulce  'yan majalissu 53 ne suka fice daga jam'iyyar ta APC mai mulki a sakamakon guguwar rikicin da ta taso a cikinta.

Ficewar wadannan 'yan majalisu daga jam'iyyar ta APC ta zo ne 'yan awoyi kalilan bayan da jami’an tsaro suka toshen gidan Shugaban Majalisar Datawan Sanata Bukola Saraki da mataimakinsa Sanata Ike Ekweranmadu.