Gwamman mutane sun mutu a gidajen yarin Kwango
April 4, 2024Mutanen sun mutu sakamakon kamuwa da cututtuka masu saurin yaduwa da kuma rashin tsafta a gidajen yarin da suka hadar da cutar tarin fuka da kuma karancin abinci harma da karancin kayan kula da kiwon lafiya, acewar jami'in hukumar kare hakkin 'dan adam.
Karin bayani:Fursunoni 900 sun tsere a Kwango
Babban jami'in hukumar a Kwango Patrice Vahard, ya ce galibin mutanen sun rasa rayukansu a gidajen yarin da ke gabashin lardin Kivu da Tangayinka, sai kuma yankin Kwilu da ke arewaci.
Karin bayani: Kotu ta daure Vital Kamerhe a Kwango
Gidajen yarin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango na daga cikin gidajen yari mafi cunkoso a duniya, acewar jami'an inda ya bada misali da dakunan masu zaman gidan wakafi da ya kamata a ajiye mutane 50 kacal, kimanin mutane 200 ke rayuwa a ciki a Kwango.