Gyaran aiyukan MDD a yankunan rikici
July 21, 2023Antonio Gutteres ya ce ya kamata a samu wata hanya ta saukake yadda majalisar ke aikin ceto a duk wurare da ake fama da rikice-rikice. Ko da ya ke wannan ba shi ne karon farko da ake irin wadannan kiraye-kirayen ba, to amma ya kasance jagoran majalisar na farko da ya yi ta nanata batun tun hawansa kujerar sakatare babban sakatare na majalisar a 2017.
Sau da dama an sha aibanta majalisar ta dinkin duniya da kauda kai akan yankunan Afirka da Asiya tare da mayarda hankali kan nahiyar Turai da sauran kasashen yammacin duniya, wannan ne ma ya sa Alkasim ke ganin akwai abunda ya kamata ita ma Afirka ta yi.
A yanzu dai nahiyar Afirka ba ta da kujera ta din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya, kuma da yawa na ganin wannan na kawo mata cikas wajen morar ababe da dama daga majalisar.
Idan har Afirka ta samu kujerar, to ita ma nahiyar za ta zama mai karfin fada a ji musamman a duk lokacin da majlisar za ta yanke hukunci kan manyan al'amura da suka shafi duniya.