1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren MDD na ziyara a Afirka

May 2, 2022

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga sojoji a kasashen Burkina Faso da Guinea da kuma Mali da su mayar da shugabancin kasar hannun fararen hula.

https://p.dw.com/p/4AhUm
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Hoto: Vladimir Astapkovich/TASS/Pool/dpa/picture alliance

Yayin da yake jawabi bayan ganawa da shugaban kasar Senegal Macky Sall a birnin Dakar a ziyarar aiki da ya fara a nahiyar Afirka, Guterres ya ce sun cimma matsayar ci gaba da tattaunawa da gwamnatocin mulkin sojin kasashen uku don ganin sun gaggauta mayar da kasashen tafarkin dimukuradiyya.

A gefe guda kuma sakataren Ma jalisar Dinkin Duniyar ya bukaci bai wa kasashen Afirka karin tallafi wanda zai ba su damar farfado da tattalin arzikinsu da ya samu tawaya sanadiyar annobar corona da kuma tasirin yakin Rasha da Ukraine, wanda a cewarsa mamayar da Rasha ta yi a Ukraine ya haifar da karancin abinci da makamashi da na kudade a kasashen Afirka da kewaye.

Ana sa ran shugaban ya kuma kai ziyara kasashen Najeriya da Nijar da kuma wuraren da rikici da ma tasirin sauyin yanayi ya shafa.