Gunnlaugsson: Ba zan yi murabus ba
April 4, 2016A cewar shugaban gwamnatin Iceland din dai, gwamnatinsa na da kyawawan aiyyuka da take gudanarwa, kuma yana da muhimmanci a barta ta karasu, kafin ba wa masu jefa kuri'u damar zaben wanda suke muradi. Sigmundur David Gunnlaugsson ya kasance kan karagar mulki tun daga shekara ta 2013, kuma sai a shekara ta 2017 ne kasar za ta gudanar da zabe.
Takardun bayanan sirrin da aka wallafa ya alakanta kamfanoni dubu 214 da wani kamfanin lauyoyi na Panama da ke gudanar da ayyukansa a asirce. Kazalika kamfanin ya kuma taimaka wa wasu masu hulda da shi, wajen safarar kudade da kaucewa biyan haraji da kuma kaucewa takunkumin kasa da kasa, acewar fitacciyar jaridar Jamus ta Sueddeutsche Zeitung.Kakakin shugaban Rasha Dmitry Peskov ya bayyana cewar, bita da kulli ne kawai ake yi wa Vladimir Putin a a wannan badakala. Duk da cewar ba'a ambaci sunan shugaban na Rasha ba, sunan wani na hannun damansa ya bulla a bayanan da jaridun suka wallafa.