Gudummowar Jamus ga Yemen
October 4, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Jamus za ta sake ɗaukar matakan agazawa ƙasar Yemen, dubi da sabuwar gwamnatin wucin gadin da ƙasar ta samu a farko-farkon wannan shekarar. A lokacin da take yiwa manema labrai jawabi bayan ganawar ta da shugaban Yemen Abd Rabu Mansour Hadi a birnin Berlin, fadar gwamnatin Jamus a wannan Alhamis.
Merkel ta yi na'am da cewar agajin da Jamus ke baiwa Yemen a shekarun da suka gabata, ba su haifar da sakamakon da ake buƙata ba ta fannin raya ƙasa, domin kuwa a cewar ta galibin ayyukan da Jamus ta bayar da kuɗin gudanar su, ba a aiwatar da su yanda ya dace ba. Akan hakane Merkel ta ce Jamus na son bayar da gudummowar inganta sha'anin Ilimi, da samar da ruwan sha da kuma kyautata rayuwar matasan ƙasar ta Yemen.
Shugaba Hadi, wanda ya ɗare kujerar shugabancin Yemen cikin watan Fabrairu dai, yana ta yin rangadin ƙasashen Turai da Amirka ne tun ranar 23 ga watan Satumba domin neman tallafin kuɗi da nufin samar da ababen more rayuwa a ƙasar sa, wadda ke fama da talauci da kuma rigingimu.
Tunda farko dai, shugaba Hadi, ya yabawa tsohon shugaban ƙasar Yemen daya gada a mulki, wato Ali Abdullah Saleh bisa rawar daya taka wajen miƙa masa mulki cikin ruwan sanyi, yana mai cewar matsalar da ake fuskanta ita ce tsohon shugaban yana da kariya daga gurfana a gaban kotu bisa laifukan da ake zargin sa da aikatawa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal