Goodluck Jonathan na ziyara a Maiduguri
January 15, 2015Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya kai wata ziyarar ba-zata a birnin Maidugurin jihar Borno mai fama da hare-haren kungiyar Boko Haram, hare-haren da a yanzu suka tabbata barazana ga zabukan Najeriyar da za gudanar cikin watan gobe a fadin kasar.
Kamar dai yadda kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya labarta, shugaban na Najeriya Jonathan, ya sauka a filin tashi da saukar jirage na birnin Maiduguri ne da karfe 3 agogon kasar, inda gwamna Kashim Shettima na jihar ya karbe shi.
Shugaban na Najeriya a baya ya yi yunkurin ziyartar Bornon bayan ziyarar sa a yankin cikin watan Maris na shekarar 2013, ziyarar da aka dage ta daga bisani, lamarin da ya janyo masa suka da caccakar sa, musamman ganin bukatar ziyartar yankin Chibok da kungiyar Boko Haram ta kwashi 'yan mata 'yan makaranta 276 a bara, abin da kuwa ya dauki hankali duniya matuka.
Daga cikin tawagar shugaban na Najeriya dai har da babban hafsan tsaron kasar Air Marshal Alex Badeh da wsu kusoshin soji game da wasu zaratan soji da basu gaza 200 ba.