1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gini: RPG na son Alpha Conde ya yi tazarce

Ahmed Salisu
August 6, 2020

Jam'iyyar RPG da ke mulki a kasar Gini ta bukaci Shugaba Alpha Conde ya tsaya mata takara domin neman wani sabon wa'adi na shugabanci a karo na uku a zaben shugaban kasa da za a yi a karshen shekara.

https://p.dw.com/p/3gWiO
Guinea Präsident Wahlen Kandidat Alpha Conde
Hoto: AP

Jam'iyyar ta RPG ta mika wannan bukata ta ce a wannan Alhamis din, duk kuwa da irin yadda al'ummar kasar ke bijirewa shirin shugaban na yin tazarce.

Kundin tsarin kasar dai ya sahalewa shugaba yin wa'adi biyu ne kacal, sai dai a baya-bayan nan shugaban na Gini mai shekaru 82 da haihuwa ya shirya wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska, wanda zai bada dama ta yin wa'adi na uku.

To sai dai 'yan adawa a kasar da wadansu kungiyoyin fararen hula da ma sauran al'umma na cigaba da tirjewa wannan batun, inda suke cewar abin da aka yi ya maida hannun agogo baya a fagen siyasar kasar.